Bazan taba yin bara ba-  inji yarinya mara hannaye biyu

Bazan taba yin bara ba- inji yarinya mara hannaye biyu

-Murjanatu Usman matashiya ce da aka Haifa babu hannaye biyu

-Yarinyar mai shekaru 15 da haihuwa ta shirya gwagwarmaya da kalubalen rayuwarta

-Yarinyar da bata da hannaye ya yarda cewa ilimi shine abunda tafi bukata ba wai bar aba wanda shine mafi ayyukan da masu nakasa ke dauka a matsayin sana’a

Bazan taba yin bara ba-  inji yarinya mara hannaye biyu
yarinya mara hannaye tace bazata yi bara ba

Murjanatu Usman yarinya ce ‘yar shekara 15 da ke zaune a karamar hukumar Bungudu dake jahar Zamfara. Duk da cewa an haife ta babu hannye biyu, Murjanatu na gudanar da rayuwarta kusan dai-dai da ta kowa.

An haifi Murjanatu Usman ba tare da hannaye ba amma tace halin da take ciki ba zai taba sata tayi bar aba. Yarinyar tace ta wadatu da  abunda iyayenta ke iya yi mata.

Duk da dai, tace tana so tayi karatu amma rashin kudi ya hana ta.

Murjanatu Usman yarinya ce ‘yar shekara 15 da ke zaune a karamar hukumar Bungudu dake jihar Zamfara. Duk da cewa an haife ta babu hannye biyu, Murjanatu na gudanar da rayuwarta kusan dai-dai da ta kowa.

“Ina yin kusan komai da ‘ya mace ke yi a gida. Ina wanka da kai na, na yi kwalliya, na sa kayana, na yi girki duk ta hanyar amfani da kafata”, ta fadi hakan a wata hira da jaridar Dailytrust ta yi da ita.

KU RANTA KUMA: Hotunan da ya tabbatar da cewa an sace yan matan Chibok

Duk da bata zuwa makaranta saboda rashin kudi, Murjanatu ta bayyana cewa tana da sha’awar karatu kuma zata iya rubutu da kafafunta.

Ta kuma ce ba ta bara,  kuma ba zata taba yi ba da yardar Allah, saboda a fadarta, ta wadatu da abunda iyayenta ke iya yi mata. Sai dai ta ce idan da za ta samu taimako, toh zata karba hannu biyu biyu. Ta ce ” Zan iya yin sana’a na taimakawa kaina, harma da sauran ‘yan uwana”.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna bukatar cewa iyaye sy tura yaransu makaranta. Kwanan nan, Gwamnan jihar Kaduna ya sha al’washin hukunta iyayen sa suka ki tura yaransu makaranta a watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel