Kwamishanan Addini yace mu ba Musulmai bane – ‘Yan Shi’a

Kwamishanan Addini yace mu ba Musulmai bane – ‘Yan Shi’a

–Yan shi’a sunce gwamnatin tarayya na shirin fito na fito da su a Jihar Yobe

–A ranar lahadi, wata gangamin rundunar sojin najeriya suka zagaye sansanin yan shi’a da ke Potiskum

–Sojin sun kasance suna tabbatar da tsaro domin kada ‘yan shi’a su tayar da tarzoma a garin

–Amma , wakilan mabiya addinin shi’a sun bada rahoton kiyayyan da ake nuna ma mutanen su a Jihar

Kwamishanan Addini yace mu ba Musulmai bane – ‘Yan Shi’a
members of the Islamic Movement in Nigeria (IMN)

Kakakin kungiyar mabiya addinin shi’a, Ibrahim Musa,ya saki wata jawabi cewa hukumar sojin najeriya na shirin wata yaki da mambobinta .

Wata bangaren jawabin tace: “A yau, 21 ga watan agusta 2016, wata gangamin dakarun sojin najeriya cike da motocin yaki akalla 5 sunyi ma sansanin kungiyar ‘yan shi’a a potiskum zobe. Bayan sa’o’I kalilan, sai suka karasa gab aba tare da tashin hankali ba. Amma ,mazauna unguwan sun kwana cikin fargaba saboda tsohon abun da zai faru da daddare .

Tabbataciyar rahoto na nuna cewa kusan kwananki goma da suka gabata sojojin sun kasance suna zagaye garin potiskum suna wakokin yaki. Tsoron kada a kawo hari aa ranar jumu’an da ya gabata bayan sallah ya sa mutane suka arce da gudu domin kare rayuwarsu. Kafin hakan.

Hakazalika, kwamishanan al’amuran addini na Jihar Yobe, Alh. Mala Musti ya kasance yana yawo hedkwatan kananan hukumomi a jihar yana jawabai cewa yan shi’a ba musulmai bane kuma kafirci suke ma aiki. Dole ne ayi kaca-kaca da su da dukiyoyin su. Hakan na nuna cewa gwamnatin jihar da shugabanni masu rawani a potiskum sun hada kai da gwamnatin tarayya domin zubar ja jinin mutanensu da suna yaki da ta’addanci.

KU KARANTA : Mabiya Zakzaky sunyi magana akan shugaban su.

Domin haka, kungiyar yan Shi’a na jawo hankalin jama’a masu son zaman lafiya da cewa rundunar sojin najeriya na shirin wata farmaki ga mutanen ta irin wacce sukayi a zaria ,watan disamban 2015. Muna da yakinin cewa gwamnati na amfani da arzikin gwamnatin domin zubar da  jinin mutane maras alhaki a kasar nan. Mambobin yan shi’a jihar yobe basu da bambanci da sauran mamabobin a wasu jihohin kasan nan.Wannan tanakudi ne a bayyana akan maganan gwamnatin tarayya cewa tana kula da hakkin yan adam . amma, tana aika rundunar sojin ta su kashe mutane ba tare da laifi ba. Za’a kama gwamnatin nan da alhakin kisa mutanen ta ba tare da hakki ba.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel