Wasu ‘yan wasan za su bar Kungiyar Man Utd

Wasu ‘yan wasan za su bar Kungiyar Man Utd

 

– Stoke City na neman dan wasan bayan Man Utd dinnan Phil Jones. 

– Dan wasa Memphis Depay zai yi zaman sa.

– An yi magana game da dan wasa Matteo Darmian.

Wasu ‘yan wasan za su bar Kungiyar Man Utd

Yan wasan Kungiyar Man Utd har kusan uku za su tashi daga Kungiyar. Sun hada da Phil Jones wanda Kungiyar Stoke City ke nema.

Mataimakin Kocin Kungiyar Stoke City, Mark Bowen ya tabbatar da cewa Kungiyar sa na zawarcin dan bayan Man Utd Phil Jones. A halin yanzu dai dan bayan mai shekaru 24 bai buga ko wasa guda ba karkashin Sabon Kocin Kungiyar Jose Mourinho. Tun zuwan Jose Mourinho dai ya rika amfani ne da Eric Bailly, Chris Smalling, Daley Blind da kuma Marcus Rojo a baya. Don haka kuwa, dan kwallon na Kasar Ingila bai buga wasa ko daya ba wannan karo.

Mataimakin Kocin na Stoke yake fadawa Jaridar Sentinel:”Ba zan manta lokacin da ya fito aka san sa ba, yayin nan Allardyce yace shi (Jones) zai gaji Duncan Edwards”. Brown yace: “Na rasa gane mai ya faru haka, Phil Jones da sani a baya Sir Alex yana magana kan sa yanzu ya zama wani abu dabam.”

KU KARANTA: MOURINHO YA BADA ARON DAN WASA

Jones dai bai buga wasa ko guda ba a Gasar Premier League na shekarar nan ta 2016/17 da Kungiyar Man Utd. Ana tunani Kocin na Kungiyar Jose Mourinho na kokarin sakin wasu ‘yan wasan domin rage yawan albashin da Kungiyar ta ke cirewa kowane wata. Har tanzu dai babu wanda ya taya Dan wasa Deepay, alamun cewa zai cigaba da taka leda a Kungiyar. Jose Mourinho na ganin cewa, zai iya sa dan wasan ya dawo da kwazo kamar yadda kowa ya san sa a PSG.

Wasu ‘yan wasan za su bar Kungiyar Man Utd

Dan bayan nan Matteo Darmian na iya tafiya, Kungiyar Napoli ta Italiya dai ta ce idan ba mai so, ita tana ciki, sai dai har yanzu Man Utd ba ta ce uffan ba. Yan wasa Mc Nair da Adnan Januzaj dai sun bar Kungiyar Man Utd zuwa Sunderland a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel