Arsenal ta koma kasuwa neman dan wasan baya

Arsenal ta koma kasuwa neman dan wasan baya

–Kunguyar Arsenal ta gaza sayen dan wasan bayan Valencia, Shkodran Mustafi

– Wenger na neman dan baya ido rufe.

– Dan wasan bayan Monaco, Marcel Tisserand ka iya zuwa Arsenal.

Arsenal ta koma kasuwa neman dan wasan baya

Bayan da zuwan Mustafi na Valencia ya ki yiwuwa, Arsenal ta koma kan wani dan bayan Kungiyar Monaco ido rufe, domin kuwa Kungiyar na fama da matsalar baya.

Bayanai sun nuna cewa, Arsene Wenger na Arsenal na shirin karo dan wasa guda daya. A baya an yi tunanin cewa Kocin zai sayo Bajamusen dan bayan nan na Kungiyar Valencia, Shkodran Mustafi, sai dai kuma abin bai yiwu ba. Kungiyar Valencia ta bayyana cewa, dan wasan ta ba na saidawa bane, don haka babu inda zai je.

KU KARANTA: ALLARDYCE NA NEMAN JOHN TERRY YA DAWO

Idan dai ba a manta ba, Dan bayan Arsenal, Per Mertesacker ya samu wani rauni da zai sa yayi jinyar watanni biyar, sannan kuma Gabriel yana fama da wani rauninn, Dan baya Gabriel ya samu wannan rauni ne yayin da suka yi wani karo da Kelechi Iheanacho a wani wasan Kungiyar da kuma Man City. Bugu da kari kuma, Laurent Koscielny ma bai da isasshiyar lafiya.

Hakan dai ya sa dole Arsene Wenger ya koma kasuwa, domin maye guraben wadannan ‘yan wasa. Kocin yake cewa: “Na karanta ba so daya ba, cewa muna kasuwa, haka abin yake. Amma kuma abin ba ya zuwa mana da sauki…” Jaridar Daily Mirror ta rahoto cewa Arsenal din na neamn dan bayan nan Monaco mai suna, Marcel Tisserand.

Majiyar ta bayyana cewa dan wasan na iya tashi don kuwa ya rasa gurbin sa a Kungiyar ta Monaco. Kwanan ma dai Kungiyar Espanyol ta Kasar Spain ta ke kokarin sayen dan wasan, Marcel Tissernad daga Kungiyar AS Monaco ta Ligue 1.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel