Damina ta yi harshe: Farashin hatsi ya soma sauka

Damina ta yi harshe: Farashin hatsi ya soma sauka

-Farashin kayayyakin abinci na yin kasa

-An soma kai kayan abincin gida a jihar Jigawa

-farashin kayan abinci ya sauka da kashi 30 a Hadejia

Damina ta yi harshe: Farashin hatsi ya soma sauka
Farashin shinkfa ya sauka da kashi 30 a Jigawa

Kafar yada labarai ta PM News ta rawaito Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN na cewa, farashin kayan abinci ya soma sauka a arewacin kasar, a inda a  garin Hadejia ta jihar Jigawa an soma kai Gero da Dawa da Shinkafa wasu kasuwanni.

A wani bincike da Kamfanini dillancin labaran ya gudanar na cewa, a ranar Talata 23 ga watan Agusta, a kasuwar Hadejia a farashin kayyakin abinci baki daya an samu rage da kashi 30 cikin dari, a inda ake sayar da buhun Gero a Naira 14,000 a maimakon Naira 18,000, buhun shinkafa ‘yar gida ana sayar da shi Naira 8,500 a maimakon Naira 11,000, haka ma buhun Dawa ya koma Naira 11,000 a maimakon 13,000, a maimakon Naira 15,000 da Naira 17,000.

Rahoton na PM News ya ci gaba da cewa, Kamfanin Dillancin labaran na Najeriya, ya rawaito cewa, bincikensa ya gano cewa, faduwar farashin sakamakon soma girbi ne, wanda ya zo daidai da kai kayayyakin gona mai yawa kasuwa, da kuma samun isashshen ruwan sama a wannan daminar.

Wasu ‘yan kasuwa da suka yi hira da wakilin kamfanin dillancin labaran sun tabbar da faduwar farashin, wani dillalin kayayyakin abincin da aka yi hira da shi ya ce farashin zai kara faduwa nan ‘yan kwanaki idan aka ci gaba da shigo da kayyakin kasuwa.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel