Rundunar Soja ta fatattaki masu garkuwa da mutane

Rundunar Soja ta fatattaki masu garkuwa da mutane

Jami’in watsa labarai na rundunar sojan kasa kanal Sani Kuka Sheka ya fitar da wata sanarwa a ranar Litinin dangane da aikin da suke yi a jihar Bauci.

Rundunar Soja ta fatattaki masu garkuwa da mutane

“runduna ta 33 na sojan kasa ta kai wani farmaki a wasu sassan jihar Bauci biyo bayan koke da al’umomin yankin suka kai na yawaitan al’amuran bata gari a yankunan.

A don haka ne rundunar ta fara yawon sintiri a ranar lahadi 21 ga watan agusta na 2016 a unguwannin Dutsen Mairama da Dogon Ruwa yankin dajin Lame/Burra forest a kanana hukumomin Toro da Ningi na jihar Bauci.

Rundunar Soja ta fatattaki masu garkuwa da mutane

Sa’annan rundunar ta kwato makamai da alburusai da dama. Rundunar zata kara kaimi wajen wajen fatattakar masu aikata miyagun laifuka a jihar da ma kasa baki daya”

Rundunar Soja ta fatattaki masu garkuwa da mutane

Asali: Legit.ng

Online view pixel