Dalilin daya sa Mourinho yaki komawa Real Madrid

Dalilin daya sa Mourinho yaki komawa Real Madrid

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya bayyana cewa saura kiris da ya koma Italy ko Sifen kafin ya zamansa kocin Manchester United.

Dalilin daya sa Mourinho yaki komawa Real Madrid

Mourinho ya fadi dalilin daya sa ba zai iya watsi da tayin horar da kungiyar Manchester United ba, ba don komai ba, sai dai don ya shiga cikin tarihin daukaka matsayin kungiyar.

“da naga dama da na tafi Italy ko Sifen. Amma gasar firimiya tana da muhimmanci matuka. “a firimiya kowa na kokarin taka rawa matuka, ba kamar suaran kasashen ba, inda manyan kungiyoyin sun mamaye sauran.” In ji Mourinho.

Sai dai Mourinho ya ce tunanin cin dukkanin wasanni a firimiya ba abu bane mai yiwuwa, amma ya nanata cewa yana baiwa yan wasan sa kwarin gwiwa sosai game da abn da kungiyar take bukata.

A baya dai Mourinho ya horar da kugiyoyin Inter Milan da Real Madrid kafin ya koma Manchester United.

Asali: Legit.ng

Online view pixel