An babbaka mutane 8 kan batanci ga Annabi

An babbaka mutane 8 kan batanci ga Annabi

Hukumomi a jihar Zamfara sun kaddamar da dokan t abaci a garin talatar mafara sakamakon tarzomar daya kaure a garin wanda yayi sanadiyyar babbaka mutane takwas.

Kamar yadda majiyar mu ta shaida mana ana zargin wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha ta talatar mafara da aka boye sunansa ne yayi kalamun batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) da kuma addinin musulunci yayin musu da ta kaure tsakanin shi da abokinsa musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta bayyana mana jim kadan da yi masa dukan tsiya, sai aka garzaya da shi zuwa asibiti, da labarin abin da ya aikata ya watsu cikin gari sai kawai jama’an gari suka harzuka, suka kai hari gidansa, kuma suka banka ma gidan wuta inda mutane 8 dake ciki suka hallaka.

Hukumar yansanda na jihar Zamfara sun sanya dokan t abaci a garin don tabbatar da zaman lafiya, kuma sunyi kira ga malaman addini da su ja hankalin jama’ansu. Shiko gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya samu halartar jana’izar mamatan.

Sa’annan hukumomin majalisar sun rufe makarantar har sai an samu zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel