Ba zan kara sayen wani dan wasa ba-Kocin Liverpool Klopp

Ba zan kara sayen wani dan wasa ba-Kocin Liverpool Klopp

 

– Kungiyar Liverpool ta sha kashi hannun Burnley.

Kocin na Liverpool, Jurgen Klopp yayi magana.

Klopp ya bayyana cewa ba zai kara sayo wani dan wasa ba.

Ba zan kara sayen wani dan wasa ba-Kocin Liverpool Klopp

Burnley ta ba Kungiyar Liverpool mamaki wannan makon, sai dai Kocin na Liverpool, Jurgen Klopp yace ba abin da zai sa ya kara sayen wani dan wasa don kuwa shi ba sakarai bane.

Jurgen Klopp na Liverpool yace, sakarci ne yayi tunanin zai kara sayen wani sabon dan wasa ba tare da shiri ba. Kungiyar ta Liverpool dai ta sha kashi wajen Kungiyar Burnley, Burnley dai sababbin shiga ne zuwa Gasar Premier League. Wannan abu ya ba kowa mamaki, musamman ganin cewa har gida aka bi Liverpool din aka doke ta.

Kungiyar Burnley ta doke Liverpool da ci biyu da nema har gidan Anfield a karshen wannan makon. Dan wasa Sam Vokes na Kasar Wales ya jefa kwallo guda cikin mintin farko da sa wasa. Andre Gomez kuma ya kara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Da aka tantabi Kocin ko zai koma kasuwa don gudun irin haka nan gaba, sai yace ba zai yi wannan sakarci ba. Klopp yake cewa: “Idan har na sake shawara bayan na rasa wasa daya kadai, to na zama sakaran gaske kenan...ba na bukatar wani dan wasa” Da ake maganar rashin dan wasan tsakiya, Kocin ya cigaba da cewa: “Emre Can na zaune bisa benci a ranar, ciwon baya ke damun sa. Haka Lucas Leiva, yana fama da rauni”

KU KARANTA: LIVERPOOL NA NEMAN DAN WASA

Kocin yace dai ya koyi darasi daga wasan, zai kuma yi kokarin ganin haka bai kara faruwa ba a gaba. Koci Klopp ya bayyana cewa bai taba tunanin cewa Burnley za ta doke su ba, yace idan da za ka fada masa kwanaki cewa irin wannan Kungiya za ta ba sa kashi, ba zai ko yarda ba. Klopp yace matsalar ba ta baya ba ce, daga yan wasan gaban sa ne matsalar ta ke.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel