Fr. Mbaka yace kada wanda ya zagi Buhari

Fr. Mbaka yace kada wanda ya zagi Buhari

-Babban shehin malamin addinin kirista wato Fr. Mbaka ya gargadi mutane game da maganganu na mugunta akan akan shugaban kasa Buhari   

- Yace shugaban kasar shi zaya biyama yan Najeriya dadadden dogon burinsu

-Yace ba’a ware Inyamurai ba

Fr. Mbaka yace kada wanda ya zagi Buhari

Shehin malamin, wanda bashi da tsoro wato Father Ejike Mbaka ya shawarci mabiyansa da su guji zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Mbaka yace shugaban kasar baiwa ne daga Allah gay an Najeriya.

A cewarsa “Tuntuni nike so na gaya maku, Allah na son Buhari. Kuma duk wanda Allah yayi ma baiwa, to karku zageshi, saboda Allah zaya tsine maku”

Premium Times sukayi bidiyon sakon nasa ga yan Najeriya a wani wa’azinsa a chochinsa.

Shehin malamin ya kara da cewa “akwai wasu muugayen mutanen dake shirin kasha shugaban kasar don su cigaba halayensu na rashawa”

Mbaka yace “Bayin Allah sunyi addu’o’I ako ina, kuma Allah ya amsa rokonmu ya bamu Muhammadu Buhari. Kuma a yau ina so na gaya maku ubangiji ya nuna mani cewa Buhari ne zabinsa. Shugaban kasa Buhari ne zabinsa ko muna sonsa ko bama sonsa. Buhari Allah ke so”.

Ya kara da cewa “ Malaman addinin kirista sunyi addu’o’i akan cin hanci da rashawa, kuma shugaban kasar nan yazo da zummzr yaki da duk abunda ke da alaka da rashawa. Kuma dukkan addu’o’inmu da mukaita yi akan rashawa Allah ya amsa ta hanyar musulmin da muke kema.”

Haka kuma dan takifen malamin ya shawarci mabiyansa kada su saurari duk wanda ke cewaan ware Inyamurai wajen jagorancin matakai a kasar nan”.

Malamin catholic ya fyede biri har wutsiya ranar Asabar 6, ga watan Agusta a wa’azinsa akan mulkin Buhari. Mbaka yace Jonathan da mutanensa suka haddasa matsalolin Najeriya, ba shugaban kasar na yanzu ba.

Fr. Mbaka yace kada wanda ya zagi Buhari

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel