Golan Barcelona ya dage kan zai koma Manchester City

Golan Barcelona ya dage kan zai koma Manchester City

Kungiyar Barcelona ta ce ta fara wata yarjejeniya da kulob din Manchester City kan komawar golanta, Claudio Bravo zuwa Man City.

Daya daga cikin shugabannin Barcelona, Robert Fernandez ya ce " Muna jiran kasancewar al'amarin a wannan makon. Muna fatan za mu samu golan da zai maye gurbin Claudio Bravo." Ana dai hasashen cewa idan har Bravo, mai shekara 33, ya je Man City, to zai mayar da golan kungiyar dan Ingila, Joe Hart, golan jeka-na-yi-ka.

Daman dai Joe Hart, mai shekara 29, yana yunkurin barin Man City tun bayan da Pep Guardiola ya zabi Willy Caballero a maimakon sa. A ranar Juma'a ne kociyan Man City, Pep Guardiola ya ce Joe Hart yana da damar barin kulob din idan har yana so. Kungiyoyi irin su Everton da Sevilla suna zawarcin golan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel