Wani ma'aikaci ya Damfari Maniyyata Zuwa Aikin Hajji 20

Wani ma'aikaci ya Damfari Maniyyata Zuwa Aikin Hajji 20

Wani Kami'in Hukumar Aikin Hajji A Jihar Nasarawa Ya Damfari Wasu Maniyyata Kusansu 30 Kudin Kujerun Aikin Hajjiin Bana..

Daya Daga Cikin Maniyyatan Mai Suna Malam Yunusa Waziri Yace Jami'in Da Kudinsu Ke Hannunshi Shine Shugaban Hukumar Alhazan, Kuma Duk Shekara Yakan Seda Kujerun Aikin Hajji Wa Jama'a.

Inda Yace A Hannunshi Sukace Fom Kuma Ko Wannensu Ya Farane Da Ajiye Naira 700,00 Inda Daga Bisani Kuma Suka Cikasa Zuwa Naira Milliyon Daya Da Dubu Hamsin.

Inda A Halin Yanzu Maniyyatan Sunce Sun Nemi Jami'in Ko Sama Ko Kasa Basu Ganshiba.

Amma Hukumar Dake Kula Da Alhazai A Jihar Nasarawan Tace Tanada Labarin Wannan Jami'i Inda Ta Bayyanashi A Matsayin Baragurbi.

Inda Ta Kara Da Cewa Ita Bazata Dauki Alhakin Salwantar Kudin Maniyyatan Ba Sakamakon Bata Hannunta Suka Biya Kudaden Nasu Ba.

Amma A Halin Yanzu Dai Jami'an Tsaro Nacan Sun Bazama Neman Wannan Dan Damfara..

Asali: Legit.ng

Online view pixel