Wenger yayi tsokaci kan siyayyan yan wasa, ya zolayi yan jaridu

Wenger yayi tsokaci kan siyayyan yan wasa, ya zolayi yan jaridu

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da jita jitan da ake yi na sabon dan wasa da zai siya.

An caccaki Arsenal na rashin yin abin a zo a gani a wannan marran na siyan yan wasa, yan wasa uku kacal kungiyar ta siya (Granit Xhaka, Takuma Asano and Rob Holding) duk da matsalar rauni da ya addabi sauran yan wasan tad a dama.

Wenger yayi tsokaci kan siyayyan yan wasa, ya zolayi yan jaridu

Jita jita na yawo cewa Wenger yayi kasa a gwiwa wajen siyan Lacazette, Draxler, Vardy, Higuain, Mustafi, Rodriguez da Mahrez.

Sai dai a yayin da yake tsokaci dangane da yan wasan da zai siya, Wenger yace “muna gab da kammala wani ciniki, ina ganin kashe kudi kawai ba tare da samun inganci ba asara ne. na fara gajiya da amsa tambaya daya kullum. Muna lura da duk abinda muke so kafin mu afka masa.”

Wenger ya yabawa sabon mai tsaron gida Rob Holding wanda ya buga wasa tare da Koscielny a wasan su da Leicester.

Yace “ban ji ana magana ba dangane da rawar da Holdin yake takawa, dan kasar ingila ne, shekarunsa 20, kamata yayi kuyi murna. Na gane ko dan bad an pan miliyan 55 bane shi yasa ba zai burge ku ba?”

Wenger ya kara da cewa “abin da yafi ci min tuwo a kwarya shine yanzu an daina tattaunawa game da kwarewan yan kwallo. Sai dai ayi ta cecekuce kan wasu abubuwa na daban, a gani na bai kamata ba”

Asali: Legit.ng

Online view pixel