Hana fim village a Kano kwangilar malamai ce

Hana fim village a Kano kwangilar malamai ce

-Malamai sun shiga siyasa da rigar addini

-Wadanda suka haramta fim su suka haramta maulidi

-Kwankwaso ya gina film village a Tiga babu malamin da ya yi suka akai

An bayyana cewa, hana gina farjiyar shirya fina-finai, da kafirta wasan kwaikwayo, da kuma shirin fim da wasu malamai suka yi, siyasa ce, kuma kwangila ce daga Abuja.

Hana fim village a Kano kwangilar malamai ce
Wasu 'Yan fim tare da Shugaba Buhari, domin sun bayar da gudunmawa maya yawa a yakin neman zabensa

Wani matashin dan kasuwa kuma daya daga cikin masu fitowa a fina-finan Hausa, Alhaji Nura Hussaini ne ya bayyana haka hirar da aka yi da shi a wani shiri na musamman a gidan radio Rahma da ke jihar a daren Lahadi 21 ga watan Augusta.

Nura wanda ya dau kimanin sa a guda yana bayyana ra'ayinsa, ya yi amfani da ayoyin Al kur'ani da Hadisi wajen kafa hujjarsa ya ce, malaman da suka kafirta shirin fim da amfani da halayyar wasu baragurbi a cikinsu, don yankewa daukacin sana’ar da kuma masu yin ta hukunci, sune wadanda suka haramta mauludin fiyayyen halitta da karatun Dala’ilulkhairat da Ishiriniya da Diwani da sauran littafan yabon Manzo Allah tsira da amincin Allahsu tabbata a gare shi.

Matashin ya ci gaba da cewa, daga Abuja ‘yan siyasa suka shirya yakar gina farjiyar shirya fina finan, domin yaki da Abdulmumini Jibrin Kofa a badakalar zargin aringizo a kasafin kudi a majalisar wakilan kasar, aka kuma hada 'yan fim da malamai domin a samu galaba, domin malaman ba su soki Kwankwaso ba a lokacin da ya ke shirya ginin farjiyar a Tiga.

A kwanan baya ne malamai suka yi tir da aniyar gwamnatin tarayya na gina farfajiyar shirya fina-finai a jihar, wanda hakan ya janyo ka-ce-na-ce, sai dai a hirar da aka yi da Malam Aminu Daurawa à shirin Ra a yi riga na BBC, a lokacin da a ke tsaka da batun, ya ce gwamnatin ba ta tuntube su ba.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel