Danganta Jonathan da Avengers mugunta ne- kungiyar ND

Danganta Jonathan da Avengers mugunta ne- kungiyar ND

-Wani kungiyar Niger Delta ya bayyana zargin da akeyi kan cewa Jonathan ke daukar nauyin Avengers a matsayin makirci

-Kungiyar yace akwai wani makircin na son kashe tsohon shugaban kasa

-ya nace kan cewa lallai Jonathan mutun ne mai son zaman lafiya

Wani kungiya, mai suna Coalition of Niger Deltans for Justice and Development ta zargi cewa akwai wani shiri da akeyi na kai Goodluck Jonathan gidan yari, a kuma kashe shi.

kungiyar tayi zargin ne bayan rahoton danganta tsohon shugaban kasa da daukar nauyin kungiyar yan ta’addan Niger Delta Avengers.

Danganta Jonathan da Avengers mugunta ne- kungiyar ND

Mr Ebiakpo Barle wadda shine shugaban kungiyar Niger Delta Justice ya bayyana cewa akwai wani makirci da ake son shirya wa Jonathan saboda a kashe shi a tsare, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 19 ga watan Augusta.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi Magana kan abunda yan arewa sukayi

Yace: “makirci da suke shirin kullawa shine su danganta shin(Jonathan) a matsayin mai daukar nauyin wani kungiyar yan bindiga a yankin Niger Delta, wato kungiyar Niger Delta Avengers. Tsohon shugaban kasan da muka sani, mutun ne mai tawali’u da gaskiya, wanda ke son hadin kan Najeriya da kuma ci gaban mutanen ta.

 “don haka, duk wani tunani da akeyi na son danganta sa da wasu mutanen banza, ko kuma cewa shi yasa ake aikata tashe-tashen bam da lalata tattalin arzikin kasa ba halin sa bane.”

Yace Jonathan ya nuna cewa shi mutun ne kuma ya sha alwashin cewa “kishina bai kai darajar jinin dan Najeriya ba kuma bana wasan siyasa da ci gaban mutanen mu ba.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel