Iyayen yan matan Chibok sun samu sako daga kun giyar Buhari

Iyayen yan matan Chibok sun samu sako daga kun giyar Buhari

-Wani kungiya magoya bayan Buhari sun roki Iyayen Yan matan Chibok da kada suyi zanga-zanga

-Kungiyar tace wannan na iya rushe ayyukan gwamnati

-An bayyana cewa shugaban kasa na aiki don ganin an dawo da yan matan a raye

Kungiyar magoya bayan Buhari a kafofin watsa labarai sun aika da sako zuwa ga Iyayen yan matan Chibok da aka sace da kuma kungiyar  #BringBackOurGirls da karda suyi zanga-zangan kamar yadda suke shiri.

Wannan ya biyo bayan wani bidiyo da kungiyar Boko Haram suka saki kan cewa a saki dakarunsu dake tsare domin su saki yan matan da suka sace, kungiyar ta bayyana kudirinta na zanga-zanga a fadar shugaban kasa.

Iyayen yan matan Chibok sun samu sako daga kun giyar Buhari
Iyayen yan matan Chibok

Muhammadu Labbo a wata sanarwa ya bukaci kungiyar da karda suyi zanga-zanga saboda wannan na iya rushe shirin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ceto yan matan.

Ya bukace su da suba gwamnati goyon baya gurin ganin an dawo da yan matan a raye. Labbo yace karda kungiyar ta BringBackOurGirls ta nuna gwamnati a matsayin mara kula kamar yadda take kokari don gannin an dawo da yan matan a raye.

KU KARANTA KUMA: Wutan lantarki ya kashe ma’aikacin KERDCO a jihar Kano

Ya bayyana bidiyon da kungiyar Boko Haram suka saki a matsayin furofaganda da nufin tilasta wa gwamnati ta saki mambobinsu.

A halin yanzu, jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa tare da kungiyar Islama na Boko Haram domin dawo da yan matan.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel