Sarkin Lagas ya aika da sako ga Niger Delta Avengers

Sarkin Lagas ya aika da sako ga Niger Delta Avengers

-Oba Riliwan Akiolu ya bayyana gamsuwa kan kokarin Buhari

-Ya roki kungiyar Niger Delta Avengers dasu samar da zaman lafiya

-Sarkin Lagas ya bayyana cewa tashin hankali bazai magance matsalar ba

Sarkin Lagas, Oba Rilwan Akiolu ya aika wasika zuwa ga mambobin kungiyar Niger Delta Avengers da su daina tashin hankali suba zaman lafiya dama a yankin. Kungiyar tayi da’awar cewa ita ta sanya bam a bututunan man petir da gas a yankin Niger Delta wanda ya shafi samar da mai da kuma tattalin arzikin Najeriya.

NAN ta ruwaito cewa sarkin Lagas yayi rokon a fadar sa a ranar Asabar, 20 ga watan Augusta lokacin bikin Isese Festival a unguwar Isale Eko na Lagos Island.

Sarkin Lagas ya aika da sako ga Niger Delta Avengers
Sarkin Lagas

Sarkin Oba Rilwan Akiolu ya bayyana gamsuwar sa kan kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dawo da dattalin arzikin Najeriya daidai.

KU KARANTA KUMA: Yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama yan bindiga uku da bam

Wasu yan makonni da suka wuce, sarkin ya shawarci Buhari kan ya daina tafiyar da gwamnatinsa a matsayin soja. Yace Buhari ya gane cewa shi ba soja bane a yanzu kuma ya dunga abu tafiyar da al’amuransa a matsayin dan farin hula, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel