ASUP ta janye shiga yajin aikin da ta shirya

ASUP ta janye shiga yajin aikin da ta shirya

Kungiyar malaman kwalejojin kimiyya na kasar nan ASUP ta janye shiga gagarumin yajin aiki na kasa gaba daya data shirya farawa ranar litinin, 22 ga watan agusta.

A jiya ne shugaban ASUP na shiyyar ‘B’ Abdullahi Yalwa ya bayyana haka a Lokoja jihar Kogi. ASUP ta janye lamarin ne bayan gwamnati ta gayyace ASUP kan teburin tattaunawa don magance matsalolin.

Duk da haka akwai yiwuwar shiga yajin aikin idan gwamnati ta kasa cimma bukatun kungiyar. Yalwa yace “akwai yiwuwar yajin aiki, idan gwamnati bata cimma yarjejeniya ba da wakilanmu wanda shugaban ASUP Usman Dutse zai jagoranta. Mun sanar da shuwagabannin jihohin mu da su zauna cikin shiri” sa’annan ya kara da nuna bacin ransa da cewa babu wani abin azo a gani da ya biyo bayan yajin aikin wata 9 da suka yi a 2013 da zai tabbatar da gyaran kwalejojin kimiyya dake kasar nan.

Yayi bayanin cewa ya zama wajibi akan kungiyar data sanar da shirin ta na shiga yajin aiki saboda rashin cika alkawurran da gwamnati ta dauka na rahoton NEEDS a shekarar 2014, ga matsalar rashin biyan albashi a kwalejojin kimiyya da dama mallakan jijohi, da kuma matsalar karancin ma’aikata.

Sauran matsalolin dake addaban ASUP sune cin mutuncin jami’an kungiyar, rashin biyan alawus din Karin girma, jan kafa wajen sake duba dokokin kwalejojin kimiyya, da kuma rashin sake zaman tattauna yarjejeniyar da aka cimma a 2010, wanda ya kamata ayi tun 2013.

“munyi hakuri matuka, don haka dole ne muyi abin da ya kamace mu a matsayin mu na kungiya. Idan ba’a magance matsalolin nan ba, dole ne mu shiga yajin aiki na bai daya” inji Muhammad Yalwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel