An tambura Legas ta ukku a jerin kaskantattun garuruwa a Duniya

An tambura Legas ta ukku a jerin kaskantattun garuruwa a Duniya

- kula da tattalin arziki sun tambura Legasgari na ukku wajen zamantakewar kaskanci

- Wannan saboda yawan barazanar da Boko Haram ke yi

- Legas ce jagaba wajen fannin al’adu da muhalli, sannan ababen more rayuwa sai dai ta karshe wajen kwanciyar hankali.

 

A jiya 18 ga watan Agusta, hukumar kula da tattalin arziki, ta fitar da wani rahoto a inda ta tambura Legas a matsayin kaskantaccen gari na ukku a wajen rayuwa.

Wannan ya nuna cewa Legas ta dawwama wajen gazawa a ma’auni na zamantakewa a dunuiya, kuma har yanzu bata haura ba tun matsayin da hukumar kula da tattalin arziki tayi mata na karshe. Sai dai kuma rahotanni na nuna cewa akwai alamun cigaban na Legas, don tana da yawan mutane fiye da miliyan 22 kuma nan da yan shekaru, zata zamo gari na 4 wajen yawa a duniya.

An tambura Legas ta ukku a jerin kaskantattun garuruwa a Duniya

A jerin matsayin, Legas ce ta 138 cikin garuruwa 140 a sahun walwala na kwanannan, a inda tafi Tripoli da Damascus, wanda a yanzu suke cikin yaki.

Ga abunda rahotan ke cewa “ Daga cikin garuruwan dake fama da talauci, 13 sun cigaba da zama baya wajen walwala. A inda suka gaza kaso 50 cikin dari tare da tsananci wajen rayuwa. Yawan barazana daga kungiyoyi irinsu Boko Haram sun kawo tsaiko wajen walwala a Legas.

A bincike na zamantakewar wurare a fadin duniya a inda suka kasa gida biyar kamarsu walwala, kula da lafiya, al’adu da muhalli, ilimi da kayan more rayuwa.

A fakaice, Legas ta zamo zakara wajen al’adu da muhalli, sannan ababen more rayuwa amma ta zamo ta kasa-kasa wajen walwala. Garuruwa ukku na Afrika da suka zamo cikin kutal wajen zamantakewa banda Legas sune Doula, Cameroon, Harare, Zimbabwe, Algiers da Algeria inda suka zamo matsayi na 132, 133 da 134 kowannensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel