Miji ya fada ma kotu matarsa barauniya ce

Miji ya fada ma kotu matarsa barauniya ce

Wani mutum da ya kai karar matarsa kotu domin a raba auren ya fada ma wani karamin kotu a Legas a ranar Alhamis 18 ga watan agusta “mata ta barauniya ce, ta sha sace min kudade, wanda hakan ke tsiyata ni.”

Miji ya fada ma kotu matarsa barauniya ce

Mutumin mai suna Livinus Uwa dan shekaru 45 wanda kuma dan kasuwa ne ya garzaya gaban karamin kotun Igando inda ya nemi a warware igiyar auren dake tsakanin shi da matarsa ta tsawon shekaru hudu, sakamakon zargin da yake yi wa matar tasa da sata.

“barauniya na aura….sata na karshe da tayi min, N350,000 ta satan min. da na kai karar ta wajen yansanda, sai ta amsa laifinta, amma bata dawo min da kudin ba.” Inji Uwa. Da yake Karin bayani, Uwa yace, matarsa Chinenye na da ya daya tare da shi. Mai karar ya kara da zargin matar tasa da bata samu halartar zaman kotun ba da cewa tana gudunsa.

Uwa ya zayyana abin da yafaru tsakanin su, inda yake cewa “tun bayan auren mu, mata ta sai ta dinga guduwa, tana dawowa. “lokacin da samu juna biyu, sai ta bace daga gida zuwa wani wurin da ban sani ba, sai bayan ta haihu ne ta dawo. “ta kara guduwa ta barni da jariri dan watanni 10, sai dai na dauko mai rainon yara ina biyanta don ta raini jaririn, da jaririn ya kai shekaru 2, sai na sa shi a makaranta, daga nan ne fat a kara dawowa.”

Bugu da kari, Uwa ya bayyana matarsa a matsayin kazama mai yawan lalaci, Uwa ya fada ma kotun “Chinenye akwai lalaci, bat a yin girki, shara ko wanki, ni ke yin dukkan ayyukan gida. “na kai kararta ga dangi na da dangin ta, kuma sun ja kunnenta amma ta ki canja halinta.”

Mutumin ya roki kotu da ta kwance igiyar auren su, inda yace “ni a yanzu bana son ta, don haka ina rokon a raba auren nan; ba zan iya cigaba da jure halin ta na sata ba.” Sai dai Alkalin kotun Adegboyega Omilola y adage karar zuwa ranar talata 20 ga watan satumba don yanke hukunci.

Misalin mako daya gabata, wani mutum mai suna Simon Akor ya bayyana ma kotu dake Nyanya Abuja cewa matarsa Patricia bata yarda ya kwanta da ita sai ya biya ta kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel