Chelsea zasu kamala sayan dan wasan Portugal.

Chelsea zasu kamala sayan dan wasan Portugal.

_ Kochin Dinamo Zagreb ya bayyana maganar sayan dan wasan.

_ Mai tsaron ragar Portugal Eduardo zai tafi Chelsea.

_ Kranjear yayi Magana akan kasuwancin.

Kochin Dinamo Zagreb Zlatko Kranjear ya bayyana cewar kungiyar Chelsea sun shirya domin siyan dan wasan Portugal. Kochin ya bayyana cewar dan shekara 33 ya shirya tsaf domin zuwa kungiyar Antonio Conte bayan wasan share fage da suka buga da Red Bull Salzburg

Chelsea zasu kamala sayan dan wasan Portugal.
Eduardo

Idan dai za’a iya tunawa Eduardo dai yana cikin yan wasan kasar Portugal da suka doka wasa a EURO 2016. Kranjera yace “ Eduardo ya samu babbar sa’a na zuwa babbar kungiya irin Chelsea, inda ya kara dacewa , Eh ina ganin dan wasan zai tafi filin wasa na Stamfordbridge bayan mun buga wasanmu da Salburg.

Mundai samu labarin cewar masu tsaron ragar Chelsea irin su Thibaat Courtois da Begovic duk anacewar zasu bar kungiyar. Haka kuma munji jita-jitan cewar Conten tana zawarcin mai tsaron ragar AC Milan wato Diago Lopez.

Asali: Legit.ng

Online view pixel