Yan daba sun harbi wani dalibin UNILAG

Yan daba sun harbi wani dalibin UNILAG

–Wani dalibin jami'ar Legas ya tsallake rijiya da baya yayinda yan daba suka kai masa hari

–An kai dalibin mai suna Bayo asibiti da gaggawa saboda harbin bindigan da akayi masa a wuya

–Shugaban jami'ar Farfesa Rahmon Bello yace jami'ar na bincike kan al'amarin

Yan daba sun harbi wani dalibin UNILAG

Wani dalibin jami'ar Legas mai karantan ilimin tattalin arzuki ya tsallake rijiya  da baya yayinda wasu mutane suka harbe shi a daren laraba, 17 ga watan Augusta.

Game da cewa rahoton Jaridar the Nation, an kai bayo asibitin koyo na jami'ar legas bayan harbin. Amma, rahoton ta kara da cewa yana cikin mawuyacin hali a asibitin akan harin da yan daban suka kai masa.

Wata majiya ta ce : “An harbi yaron ne a wuya, sunyi niyyar harbin shine a kai.”  Majiyar tace yaron mazaunin sansanin Biobaku ne kuma kila dan daba ne shima. Shugaban jami'an, Farfesa Rahamon Bello yace ana gudanar da bincike.

KU KARANTA : Daliban jihar Kano a Sudan da India na cikin tsaka mai wuya

“Na samu labarin kuma muna tunanin yan daba ne. Muna yaki da sy. Jami'an tsaro da yan sanda na gudanar da bincike. Yaron ya rayu. An kaishi asibitin LUTH . yan daban sunyi harbinshi a kai,amma ya ci sa'a.” , ya ce

Wannan harin ya farune kwanaki kadan bayan wani dalibin jami'ar mai sunaOdusami Ajibola Matthew, dan ajin karshe ya mutu bayan buga kwallon kafa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel