Kano tayi akaunta ta farko bayan shekara 49

Kano tayi akaunta ta farko bayan shekara 49

-An nada Aisha Bello Muhammad a matsayin akanta ta jahar.

-Itace mace ta farko da aka taba nadawa a matsayi a tarihin jahar Kano.

-Kafin nadata da akayi,itace kwamishinar kasafin kudi da tsare-tsare na jahar.

Kano tayi akaunta ta farko bayan shekara 49

Gwamnan jahar kano dakta Abdullahi Ganduje, ya bada damar a nada Aisha Bello Muhammad a matsayin akanta ta jahar . kamar yadda jaridar leadership ta bayyana, Aisha Bello Muhammad it ace mace ta farko da aka nadawa a matsayin a shekara 49 na tarihin jahar.

Muhammad Garba komishinan watsa labarai, aciki bayanin shi yace “Nada Aisha Muhammad yazone gadan gadan”. Shikuma mai kula da ofishin na akanta Ibarahim kura yakoma matsayinsa na daracta na ma’adani, kafin nadata, itace komishinan kasafin kudi da tsare tsare na jaha.

Aisha Muhammad wadda aka Haifa 1965 digiri a fannin aikin ma’aikata dakuma fannin kudade. Ta rike matsayi daban daban harda manaja a bakuna daban daban wanda ya hada da manajan bakin First bank dake karamar hukumar kaduna ta kudu dakuma manajan dake kula da aiyuka na bankin dake da reshe a minna, sannan kuma shugaban kula da hatsarin bada bashi a bankin habib.

Idan zaku iya tunawa mace ta taba kafa tarihi na zama shugaban dalibai na jami’a a yankin.  Daliba Amina Yahaya, yar shekara ta karshe mai karatun turanci a jami’ar sokoto ta zama shugaban dalibain jami’ar wanda maza ne akasan suke samun mukamin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel