Abinda na tattauna da buhari - Abdus salam Abubakar

Abinda na tattauna da buhari - Abdus salam Abubakar

–Shugaba Muhammadu Buhari yayi babban bako a fadar shugaban kasa yau, Abdusalami Abubakar

–Sunyi wata ganawar sirri a ofishin shugaban kasa

–Abubakar yace sun tattauna ne akan matsalolin da suka shafi kasa

Abinda na tattauna da buhari - Abdus salam Abubakar

Tsohon shugaban Kasa, Janar Abdusalami Abubakar (mai ritaya) yayi wata gajeruwar ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa,a Abuja a ranar Alahamis,18 ga watan Augusta. Yayinda yake Magana a karshen ganawar, Abubakar yace sun tattauna wasu abubuwa ne dasuka shafin kasa da kuma kasashen waje.

“Na zo ne domin tattauna wasu abubuwa ne dasuka shafin kasa da kuma kasashen waje. Na tattauna da wanda na zo gani, kuma bani tunanin in tattauna kuma da yan jarida.

Tsohon shugaban kasan yaki bayyana hakikanin abunda suka tattauna. Yayinda yake Magana a zancen cewa yayi ko oho da al’amuran da suka shafi kasa, Abubakar yace yayi Magana da wadanda ya kamata yayi Magana dasu.

Game da cewar sa, kwamitin zaman lafiyan zaben 2015 suna aiki domin tabbatar da zaman lafiya a kasan . Yana kira da yan najeriya da su baiwa gwamnatin shugaba buhari goyon baya a yunkurin shi na fuskantar kalubalen kasa.

KU KARANTA : An kashe ‘yan Boko Haram 27 a wani gari kan iyaka da Kamaru

Wannan ganawar yayi kama da ganawar da shugaba buhari yayi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar laraba 3 ga watan augusta. Yayinda yayi Magana da shi kimanin mintuna 20, jonathan yace ya gana da buhari ne domin yi masa Magana akan wasu abubuwan da suka shafi wajen Najeriya.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel