Hukumar KAI ta kama masu talla 46 a Legas

Hukumar KAI ta kama masu talla 46 a Legas

–Ma’aikatan hukumar yaki da rashin dabi’a a Jihar Legas sun kama masu talla a titi 46

–An damke masu baran ne a wurare daban-daban a jihar saboda laifin janyo cinkoso a manyan titunan Jihar Legas.

Hukumar KAI ta kama masu talla 46 a Legas

Ma’aikatan hukumar yaki da rashin dabi’a a Jihar Legas watau Kick Against Indiscipline (KAI)   sun kama masu talla a titi 46

An fara kamasu ne bayan gwamnatin jihar legas ta zantar da wani doka na cewan duk wanda aka kama ya sayarda ko sayan abu a bakin titi zai kwashe watanni 6 a gidan yari ko kuma ya bisa fansan 90,000 kuma mutane da dama sun ki hakan

Jaridar the nation ta bada rahoton cea an kama masu tallan ne a unguwannin Maryland, Ikeja, da Mobolaji a jihar tsakanin karfe 4-6 na yamma . Sun kara da cewa an gurfanar da su a kotun Samuel Ilori da ke Ogba ,Jihar Legas.

KU KARANTA : An raunata yar zaman shago a kan naman N400

Wata jawabin da jami’an  hulda da mutane na hukumar, Rahmat Alabi tace kamen da akayi na bisa gay akin da takeyi na hana saye da sayarwan kayayyaki musamman a wuraren da aka haramta a jihar. Tace anyi kamen ne kuma saboda a kan tauna tsakuwa domin baiwa aya tsoro, da kuma nuna ma mutane cewa tallace-tallace a wuraren na da hadari.

Hukumar ta lashi takobin kama duk wadanda suka sabawa dokan da aka saka.Shugaban hukumar kuma CSP Amusat Jimoh tace : za’a dau matakai masu tsauri akan masu saba doka a Jihar.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel