Wani dan sanda ya saka hoton batanci na Jonathan a fesbuk

Wani dan sanda ya saka hoton batanci na Jonathan a fesbuk

Wani dan sandan Najeriya mai suna Adeojo Lanrewaju Manlarry ya saka wasu hotunan batanci na tsohon shuganan kasar Najeriya Goodluck Jonathan a shafin sa na fesbuk.

Shi dai dan sandan ance dan jihar Ekiti ne amma kuma yana aiki ne a jihar Kogi. Dan sandan ya saka hotunan na tsohon shugaban kasar Jonathan ya rataye kansa a jikin wani icce tare kuma da matar sa Patience Jonthan tana ta rusa kuka a gaban sa.

Ga dai hotunan nan kasa:

Wani dan sanda ya saka hoton batanci na Jonathan a fesbuk

A tare da hotunan kuma sai dan sandan ya rubuta cewar: "Da jin kunya kara mutuwa". Yanzu haka dai dan sandan ya cire hotunan bayan da jama'a da yawa suka bayyana rashin dacewar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel