Hukunci 5 da za'ayi wa Sanatoci da yan majalisar wakilai da aka kama da laifi

Hukunci 5 da za'ayi wa Sanatoci da yan majalisar wakilai da aka kama da laifi

A lokacin da labari yazo na cewa Gwamnatin Tarayya tana shirin tallafa wani hukunci na kashe mayaka a fadin kasar a matsayin horo, an kafa muhawara, yayinda wasu suka amince da ra’ayin, wasu da dama sun kafa alamar tambaya kan ra’ayin.

Hukunci 5 da za'ayi wa Sanatoci da yan majalisar wakilai da aka kama da laifi

Mayakan Niger Delta wadda sune farkon wadanda aka fuskanta kan wannan yunkurin, wasu sunce suna “fada ne kan yancin” mutanen su. Hujjar su shine cewan laifukan da mayakan suka aikata yazo ne sakamakon sakaci da kuma yunwa da mutanen suke fama da shi.

Har ila yau, wasu sun yi tambaya kan cewa abunda ya kamata ayi ma jami’an gwamnati masu aikata cin hanci da rashawa wanda sun taimaka sosai gurin halaka kasar nan.

Wadanda ya kamata su yi biyayya, kuma su kafa doka, sun zama sune suka fi kowa karya doka.

KU KARANTA KUMA: Taron PDP: Bamu san me zamuyi ba – INEC

Ga abubuwa 5 da ya kamata ayima Sanatoci, yan majalisar wakilai da dukkan jami’an gwamnati wadanda suka aikata muggan laifuka kamar mu a kasa:

1. Takardan sallama daga aiki

Wannan mataki mai kyau ne, a salami yan majalisa da aka kama da laifi, amma kasar mu ta zama matatarar cin hanci da rashawa. Da wuya ka ga an salami yan majalisar Najeriya koda kuwa an kama su da hujjar aikata hakan, za’a samu hanyar warware wa.

2. Hutu

Hutu wata hanya ce da za’a iya bi don magance cin hanci da rashawa da yayi katutu a tsakanin yan majalisar Najeriya.

3. Daskarar da asusun su a kuma kwace dukiyoyinsu. Amma asusunawa ka san suna amfani da? Ya maganar kudaden da suke ajiyewa a manyan tankoki? Gidaje nawa kasan sun mallaka? Gidajen dake dauke da sunayen tattaba kunnen su da ba’a riga an Haifa ba ma.

4. Ayi masu zindir a kuma duke su, a tunanin wasu wannan ya mayar damu zamanin da kuma ya zama Kaman daukar hukunci a hannu. Duk da haka, wasu sun amince kan cewa idan aka aikata hakan akan dan majalisa daya, zai zama darasi ga sauran.

5. Hukuncin kisa

An samu muhawara kan hukuncin kashe jami’an da suka aikata cin hanci da rashawa na dan wani lokaci. Bisa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘idan bamu kashe cin hanci da rashawa ba, cin hanci da rashawa zai kashe mu.’

Asali: Legit.ng

Online view pixel