Wani Attajiri na Kasar Japan yayi alkawarin $30,000 ga ‘yan wasan Najeriya

Wani Attajiri na Kasar Japan yayi alkawarin $30,000 ga ‘yan wasan Najeriya

 

– Wani hamshakin Attajiri na Kasar Japan yayi alkawarin $30,000 ga ‘yan kwallon Najeriya idan har suka ci gwal.

– Katsuya Takasu yace zai ba su kyautar $20,000 idan suka ci zinari ko kuma $10,000 idan suka ci tagulla a Gasar.

– Hukumar kwallon Kafar Kasar Najeriya tace wannan duk ba zai dauke ma ‘yan wasan ta hankali ba.

Wani Attajiri na Kasar Japan yayi alkawarin $30,000 ga ‘yan wasan Najeriya

Wani gawurtaccen mai kudi a Kasar Japan yayi alkawarin $30,000 ga ‘yan kwallon Najeriya idan dai har suka samu lashe lambar gwal a Gasar Olympics.

Wani likita kuma hamshakin attajiri mai suna Katsuya Takasu ya wa ‘yan kwallon Najeriya alkawarin kyautar $30,000 idan har suka ci gwal a Gasar Olympics na RIO 2016. Dakta Takasu bai tsaya nan ba, ya kuma yi alkawari $20,000 idan har Kasar ta samu lambar zinari ko kuma $10,000 idan ta zo na uku, ta ci tagulla a Gasar.

BBC ta rahoto cewa Attajirin yayi wannan alkawarin ne bayan da ya ji halin da ‘yan wasan Kasar suke ciki. Katsuya Takasu yace: ’Na karanta labarin halin da ku ke ciki na rashin kudi, don haka nace bari in bada gudumuwa ta. Ba kuma ina yi bane don duniya ta sani, sai dai kawai don ku kara hazaka. Kungiyar Najeriya ta burge ni, ku dub, duk da wannan matsalar sun kai mataki mai nisa a wannan Gasar.’ Takasu ya cigaba da cewa dai: “Ko sun ci, ko ba su ci ba, zan basu wani abu, saboda rashin alawus din su da (wanda ba a biya ba)”

KU KARANTA: KUNGIYAR WARRI WOLVES TA NAJERIYA NA NEMAN BALOTELLI

Mataimakin Shugaban Hukumar kwallon Kafar Kasar ta Najeriya, Seyi Akinwunmi yace sun gode da wannan abin kirki na Takasu, sai dai kuma fa ba wannan ke gaban su ba, kuma mutuncin Kasar Najeriya ne kan gaba.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel