PDP ta kara wa'adin mulkin Makarfi da watanni 12

PDP ta kara wa'adin mulkin Makarfi da watanni 12

Babbar jam'iyya mai adawa ta PDP a kasar Najeriya ta sanar da karin ma'adin mulkin shugaban kwamitin rikon kwaryar ta Senata Ahmed Makarfi har na tsawon watanni 12.

PDP ta kara wa'adin mulkin Makarfi da watanni 12

Jam'iyyar ta PDP dai ta cimma wannan matsaya ne bayan da manyan jiga-jigan jam'iyyar suka kammalla wani babban taron masu ruwa-da-tsaki a gidan gwamnatin jihar Rivers.

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnoni a karkashin jam'iyyar, yan majalisun tarayya da sanatocin jam'iyyar dama dukkan shugabannin jam'iyyar a daukacin jihohi 36 na kasar.

Rahotanni dai na nuna cewar mataimakin shugaban sanatocin kasar Ike Ekweremadu da kuma gwamnan jihar Ribas sune suka fara gabatar da kudurin na karin wa'adin yayin da kuma sauran wadan da ke halartar taron suka amince.

Hakanan kuma jam'iyyar tace zatayi anfanin da wannan lokacin da aka dibar wa kwamitin don ganin ta sasanta da bangaren Ali Modu Sheriff.

A nashi bangaren kuma, shugaban kwamitin na wuci gadi Sanata Makarfi ya anshi sabon wa'adin da aka basu sannan kuma yayi alkawarin cewar ba za a ji kunya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel