Me ka sani dangane da lambobin Gasar Olympics?

Me ka sani dangane da lambobin Gasar Olympics?

 

– Ba wai zallar Gwal bane a lambar da ake ba wadanda suka zo na daya a wasa.

– A cikin lambar gwal din da ake ba guraru ana hadawa da akin karfe.

– Michael Phelps ne wanda ya fi kowa lambar gwal a tarihin Olympics, yana da guda 23.

Me ka sani dangane da lambobin Gasar Olympics?

 

 

 

 

Yanzu haka ana Gasar Olympics a Birnin RIO na Kasar Brazil, an saba raba kyautar lambar gwal, azurfa ko zinari ga wadanda suka zi na daya, biyu da na uku.

An kusa kammala Gasar Olympics na Rio 2016, ‘yan wasa da dama sun samu lambobi na kyauta wanda ya kama da gwal, azurfa da kuma tagulla, wasu kuma na kan ci. Babu Kasar da ta kai Amurka cin gwala-gwalai a Gasar Olympics, Russia da Kasar Sin (China) na biye. Har Yanzu dai Najeriya ba ta ci komai ba a Gasar Olympics na RIO 2016 tukun, sai dai ana sa ran hakan. Ko da me ake hada wadannan karafa?

Ana sanya kamar giram (gm) shida watau (6gm) na tsantsar gwal a cikin lambar gwal din da ake ba ‘yan wasan da suka zo no daya, darajar sa ba zai wuce £200 ba.

 

KU KARANTA: YAR TSEREN NAJERIYA TAYI GABA A GASAR OLYMPICS

Nauyin Lambar gwal din na kaiwa giram 500 (500gm), mafi yawa dai zinari ne ake sauyawa, asalin gwal a ciki bai wuce kashi 1% (Cikin 100), lokacin da aka bada kyautar asalin gwal shine Gasar Olympics na shekarar 1912 da aka yi a Birnin Stockholm na Kasar Sweden.

Ana daukar kwana biyu wajen hada wadannan lambobin, wani kamfani a Kasar da ke kusa da Garin Rio ke wannan aiki na kera karafuna har 5,130 na Gasar.

Zinarin da ake sawa cikin lambar gwal mafi yawo ana samo sa ne daga madubai da wasu tarkacen.

Michael Phelps ya fi kowa lambar gwal a tarihi, yana da 23, a mata kuma Larisa Latynina ce kan gaba.

Tun daga shekarar da aka fara Gasar 1896, babu Gasar da Kasar Birtaniya ba ta ci gwal ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel