Bitar wasu muhimman labarun Naij.com na ranar Talata

Bitar wasu muhimman labarun Naij.com na ranar Talata

Ga wasu muhimman labarai da muka kawo muku a ranar Talata 16 ga watan Agusta, ko mai karatu ba samu damar karantawa ba.

Bitar wasu muhimman labarun Legit.ng na ranar Talata
Tsageru Niger Delta

Tashin Hankali: sama da tsageru 100 sun mamaye fadar gwamnatin Akwa Ibom

Wasu tsageru kimanin su 100 suka mamaye fadar gwamnatin jihar Akwa Ibom a wata mummunan tarzoma da ta haifar da tashin hankali a babban birni jihar.

Kai ba soja ba ne a yanzu a cewar Sarkin Lagos ga shugaba Buhari

Babban basaraken jihar Lagos Oba Riwan Akiolu, ya shawarci Buhari a kan salon mulkinsa wanda ya yi kama da na soji. Don haka ya sani cewa shi yanzu ba soja ba ne.

Bitar wasu muhimman labarun Legit.ng na ranar Talata
Oba Akioulu da gwamna Ambode da kuma Tinubu

Mataccen kwado a cikin robar ruwa sha

Wata ‘yar wasan fina-finan Nollywood ta sa wani hoton bidiyo a shafinta na Instagram na wani mataccen kwado a robar ruwan shan da ta saya.

Bitar wasu muhimman labarun Legit.ng na ranar Talata

Ina fatan komawa Chelsea da lambar zinare –Mikel

Mikel John Obi dan wasan tsakiya na Chelsea kuma Kyaftin din kungiyar kwallon Nigeria a wasan Olympics ya ce burinsa ya koma kulop din da lambar zinare daga wasan na Rio.

Dan kwallon kafan Nigerie a Azerbaijan ya mutu

Micheal Umanyika wani dan Nigeria mai bugawa Zagatala PFK a Kasar Azerbaijain ya mutu a yayin da ya ke atisaye da kulop din a ranar Litinin 15 ga watan Agusta.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel