Shahararrun yan kasuwar yanar gizo sun shirya haduwa a Legas.

Shahararrun yan kasuwar yanar gizo sun shirya haduwa a Legas.

Ranar 26 ga watan Agusta, yan kasuwar yanar gizo na Najeriya zasu hadu su tattauna akan harkokin kasuwanci da cinikayya, a wani hotel na Intercontinental dake Legas, wannan shine taro na farko na kasa da kasa akan kasuwanci ta hanyar yanar gizo.

Shahararrun yan kasuwar yanar gizo sun shirya haduwa a Legas.

Legit.ng sun dauki nauyin daya daga cikin dadaden shagulgulan kasuwanci na wannan karon. zamu kawo muku zakakuran kasuwannin Najeriya dake yanar gizo, irin su Jumia, Dealday, HotelOga, Yudala da Jiji.ng su gaya muku abun da sukeji na kasuwanci ta hanyar yanar gizo wanda shikeci anan kasar.

An kiyasta kaso 25 cikin 100 na kasuwanci ta hanyar yanar gizo yana bunkasa a shekara, wanda hakan ya bunkasa tattalin arziki daba saina mai ba zuwa matsakaici ko dogon zango. Hakan kuma ya taka muhimmin rawa saboda kanana da matsakaitan sana'o'i suna amfani da kafofin sadarwa na komfuta domin su tallata hajarsu da "Afirika keyi" da ra'ayoyinsu na cinikayya.

Taron zaya hada da gogaggu don musayyar ra'ayi, tattaunawa dakuma nemo mahimman hanyoyi dazasu habbaka cigaban kasuwanci na yanar gizo a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel