Mahaifiya ta jefar da tagwayen ta a rafi

Mahaifiya ta jefar da tagwayen ta a rafi

Yadda mata da yawa ke neman Allah ya azurtasu da yara, wasu kuma Allah ya basu amma basu san muhimmancin hakan ba, kana jefar da su ma suke yi.

Mahaifiya ta jefar da tagwayen ta a rafi

Game da Jaridar Punch, jami'an yan sanda jihar legas sun fara gudanar da bincike akan mutuwan wasu tagwaye, Wadanda aka ga gawan su a wata rafi kusada gidan mai a Unguwar Ajangbadi sa ke jihar a ranan juma'a, 12 ga watan Augusta.

Ayarin mazauna unguwar sun taru suna daukan hotunan jaririran  kafin zuwan jami'an yan Sanda. Bayan sunga tagwayen , yan sandan sun kira Environmental Health Monitoring Unit domin dauke gawan kuma kaisu dakin ajiye gawawwaki.

KU KARANTA : Jarirai 12 sun mutu sanadiyar gobara cikin asibiti

Wata majiyar yan sanda ya bayyana cewa, yayi mamakin yanda mazauna unguwar sukayi ko oho yayinda suka ga gawawwakin, ya kara da cewa tagwayen sun mutu kafin zuwan yan sanda.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel