Sojoji sunyi barazana ga mutane uku da ake nema don sabon bidiyon yan matan Chibok

Sojoji sunyi barazana ga mutane uku da ake nema don sabon bidiyon yan matan Chibok

-Sojojin Najeriya sun aika da barazana mai sanyi ga mutane uku da ake nema kan sabon bidiyon yan matan Chibok

-An ce mutane biyu daga cikin mutun uku da ake nema basu ba sojoji hadin kai ba

Sojojin Najeriya sun bayyana cewa Ahmed Bolori da kuma Aisha Wakil, biyu daga cikin mutanen da sojojin Najeriya suka bayyana neman su ruwa a jallo a ranar Lahadi saboda alakarsu da yan kungiyar Boko Haram sun ki ba da hadin kai.

Sojoji sunyi barazana ga mutane uku da ake nema don sabon bidiyon yan matan Chibok
Ahmes Salkida
Sojoji sunyi barazana ga mutane uku da ake nema don sabon bidiyon yan matan Chibok
Aisha Wakil
Sojoji sunyi barazana ga mutane uku da ake nema don sabon bidiyon yan matan Chibok
Ahmed Bolori,

Wata sanarwa daga sojojin a ranar Litinin, 15 ga watan Augusta sunce: “Don Allah ku lura cewa (sic) sun kasa bamu Karin haske kan lamarin,” ance sanarwan yana dauke da sa hannun kakakin sojojin Najeriya Col SK Usman, ya kara da cewa, suna kinibibi. Suna so komai ya kasance bisa sharudansu.

Ba tare da sun fadi komai ba dangane da haduwarsu da Bolori da Wakil, wanda dukka suka bayyana son bayar da hadin kansu ba, sojojin sunyi barazana, cewa suna son komai ya kasance bisa sharudansu.

KU KARANTA KUMA: Wike ya maida martani ga zargin Ali Modu Sheriff

Bisa ga Sahara Reporters, mutun da uku da ake nema shine, Ahmed Salkida, wani dan jarida, yana kasar Dubai, tare da Iyalinsa.

Ba’a ba da wani bayani game da shi a sanarwanba, amma ya nemi sojojin da su dauki nauyin dawowarsa gida ta hanyar tura masa takardan gayyata da kuma katin jirgin sama.

Jaridar Premium Times ta ruwaito a da cewa anga Aisha Wakil, lauyan Najeriya da sojojin Najeriya suke nema a Hedkwatan tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel