Kungiyar Kristoci ta Najeriya ta dargaje

Kungiyar Kristoci ta Najeriya ta dargaje

-Shuwagabannin kungiyar kristocin Najeriya (CAN) na takaddama kan shugabancin Supo Ayokunle

-Ana zargin tsohon shugaban kungiyar CAN Pasto Ayo Oritsejafor, da hannu cikin fashewar kungiyar

-Kristocin Arewa na shirin kikiro tasu kungiyar da helkwata a Abuja

Takaddamar siyasa  da ta addabi Kungiyar Kristocin Najeriya CAN ta jaza ficewar 'ya'yanta daga arewacin kasar daga jam'iyyar.

Kungiyar Kristoci ta Najeriya ta dargaje
fasto Ayo Oritsejafor

Kungiyar CAN wadda itace babbar kungiyar kristocin kasar ta shiga matsaloli domin zargin da ake mata na tsoma kanta cikin siyasar kasar tare da rigingimun shugabancin ta

Shiyyoyi 19 na jihohin Arewa na kungiyar sun ki amincewa da sabon shugaban Reverend Supo Ayokunle, suna cewa tsohon shugaba Pasto Ayo Oritsejafor yayi kutukutun zaben shi. Ana zarginsa da ware kristocin Arewa yayin zaben da ya kawo Ayokunle. Ba'a ji ta bakinsa ba, amma kristocin kudu na kasar su karyata zargin magudi a zaben

Shiyyoyi 17 na gungiyar daga kudancin kasar ta bakin sakataren kungiyar Dr Joseph Ajujungwa, suna cewa ba wani rikici a kungiyar, suna kuma karyata kalaman limaman na Arewacin kasar.

KU KARANTA : Fasto ya kasha wata mata a cikin coci

A wani jawabi daga kungiyoyi biyu na kristocin Arewa wanda Reverend Luka Shehu, da Hon Peter Luka suka sa ma hannu daga Jos, jihar Plateau suna mai cewa "rashin adalci, algushu da karairayi" wadanda suka kawo Ayokunle suka jaza matakin da suka dauka na komawa ga kungiyar kristocin Arewacin Najeriya (NNCA) wadda ke akwai kafin samun mulkin kai. Suka ci gaba da zargin shuwagabannin kungiyar da kasa bayyana yadda akayi da biliyoyin  naira da aka ba CAN daga cikin gida da kuma waje.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel