Ba zakayi kudi ba da bugawa kasar Najeriya kwallo inji Okocha   

Ba zakayi kudi ba da bugawa kasar Najeriya kwallo inji Okocha  

Tsohon jagoran tawagar kwallon kafa ta kasar Najeriya watau Super Eagles Jay Jay Okocha yace kada ma yan kwallon Najeriya su sa ran cewar zasu iya yin arziki da bugawa kasar kwallo ba.

Tsohon dan wasan ya fadi hakan ne yayin da yake tsokaci game da cece-kucen da ake tayi dan gane da kudaden garabasar yan wasan da kasar Najeriya ta hana su ne. Okocha yace kamata yayin yan wasan su manta da wadannan kudin kawai su cigaba da maida hankali da aiki tukuru don ganin sun yi nasara.

An dai ruwaito dan kwallon yana cewa: "Kar ma wani dan kwallo yayi tunanin zai yi kudi don ya bugawa kasar kwallo. Kamata yayi yan kwallon su kauda hankalin su daga kudaden da suke tunanin samu su buga kwallon dan kishi da sha'awa kawai."

Okocha dai ya buga kwallo a kungiyoyi da dama da ma kasar Najeriya ciki har da Eintracht Frankfurt (Germany), PSG (France), Fenerbache (Turkey), Bolton, Hull City (England) at club level.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel