Kumallon mata: Wata mata ta takaita dan kishiyar ta da mugun bugu

Kumallon mata: Wata mata ta takaita dan kishiyar ta da mugun bugu

Rundunar yan sanda sun kama Wata muguwar mata a bisa nakasa dan kishiyar ta.

Rahotannin da ke zomana suna nuni ne da cewar ita dai matar mai suna Fatimoh Olanrewaju ta shiga hannun jami'an tsaro ne dake yaki da safarar mutane da hadin gwiwar yan sandan sashen jihar Ogun a ranar Alhamis din da ta gaba ta.

Kumallon mata: Wata mata ta takaita dan kishiyar ta da mugun bugu

Kumallon mata: Wata mata ta takaita dan kishiyar ta da mugun bugu
Source: Getty Images

KU KARANTA: Saraki yayi wa Buhari wankin babban bargo

Jami'an tsaron suka kara da cewa ita matar daman ba tun ranar ba ta saba muzgunawa dan kishiyar nata duk kuwa da yadda magabatan yaron suka rika shiga tsakanin su.

Shi dai dan kishiyar wanda ake kira Iyanu yanzu haka yana babbar asibitin tarayya ta garin Ogun din inda yake jinyar ciwuka da kuma karayar da yasamu saka makon bugun da kishiyar uwar tasa da tayi masa.

A wani labarin kuma shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba fa mutum nagari mai gaskiya ba ne kamar yadda ake ta kururuwa a kan sa. Saraki ya ce gwamnatin Buhari gwamnati ce ta mahandama da kuma wawurar kudaden jama’a.

Legit.ng Hausa ta samu cewa da ya ke jawabi a Gidan Talbijin na Channels, a matsayin Saraki na Darakta Janar na Kamfen din Atiku, ya ce Buhari ya rungumi masu kashi a gindi ya goya, don haka kimar sa da kallon da ake yi masa na mai gaskiya, ta zube a kasa warwas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel