Wani mahaifi ya gane yarinyar shi a bidiyon

Wani mahaifi ya gane yarinyar shi a bidiyon

–Wani mahaifi ya gane ‘yar shi a bidiyon da kungiyar Boko Haram ta saki nay an matan Chibok

–Mutumin mai suna Kanu Yakubu, yace yarinyar shi mai sun Maida Yakubu , ce tayi Magana a madadin sauran yan matan a cikin bidiyon.

–Yakubu yace yanada yakinin cewa ya gane yan mata 10 cikin yan matan chibok din

Kanu Yakubu, mahaifin daya daga cikin yan matan chibok ,yace ya gane ‘yar si a cikin bidiyon da yan kungiyar tada kayar Boko Haram ta sake a ranar lahadi 14 ga watan Agusta.

Game da Yakubu, yarinyar shi wani dan kungiyan boko haram ya kira ta gabatar da kanta a cikin bidiyon. Maida Yakubu ta fada bidiyon cewa ita yar asalin garin Chibok ce kuma daya daga cikin yan matan da akayi garkuwa da su a makarantan gwamnatin mata da ke chibok. Yarinyar tace kimanin shekara 2 kenan ana rike da su. Maida yakubu tace rundunar sojin saman gwamnati sun kashe wasu yan matan.

Wani mahaifi ya gane yarinyar shi a bidiyon
maida yakubu

Mahaifin ya fada ma manema labarai a abuja  cewa: “Da naji muryan ta, na gane cewa yarunya ta ce. inada yakinin cewa ya gane yan mata 10 cikin yan matan chibok din.

Kakakin kungiyar BBOG, Abubakar Abdullahi ya fadi a ranar lahadi cewa an gane akalla mutum daya cikin yan matan chibok din.

“Munada yakinin cewa yan matan chibok ne , Mun gane kimanin mutane 10 daga cikin su ta bidiyon

Abdullahi ya fada ma AFP.  Abdullahi yace yana sauraro gwamnatin tarayya da kuma iyayen yaran kafin ya saki wasu sunaye.

KU KARANTA :Bitar wasu muhimman labarai na ranar Litinin a Jaridu

Yan kungiyan tada kayar bayan sun saki wata sabuwar bidiyo a ranar asabar ,13 ga watan augusta wanda ke dauke da yan matan chibok sanye da hijabi kimanin su guda hamsin(50). A wannan bidiyo, wani dan boko haram rufe da fuska ya bada sako zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari akan cewa gwamnatin tarayya ta saki wasu yan boko haram da jami’an tsaro suka kama a matsayin fansan yan matan Chibok. Har yanzu suna rike da kimanin yan mata 200 cikin 276 da sukayi garkuwa dasu a watan afrilun 2014.

Asali: Legit.ng

Online view pixel