Kiristoci sunfi yan ta’adda aikawata laifi - Sultan

Kiristoci sunfi yan ta’adda aikawata laifi - Sultan

-Sa’ad Abubakar na III, Sultan na Sokoto ya kare sanya hijabi

-Sultan yace sanya hijabi wani gata ne ga dukkan Musulmai

-Sa’ad Abubakar na III yace Kiristoci sun fi yan ta’adda aikata mugayen laifuka

Kiristoci sunfi yan ta’adda aikawata laifi - Sultan
Sultan na sokoto tare da gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole

Sultan na jihar Sokoton Alhaji sa’ad Abubakar na III ya bayyana cewa duk da cewan ba’a yarda cewan Kiristoci yan ta’adda bane amma suna aikata mukayen laifuka ga dan Adam.

Sa’ad Abubakar na III yayi Magana a babban birnin Benin a taron majalisa na kungiyar Nigeria Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA).

Abubakar ya yaba ma kungiyar da sukayi sanarwa mai karfi dake kare addinin Islama a matsayin addinin zaman lafiya. A kan maganar sanya hijabi, ya bayyana cewa sanya hijabi hakki amma ba dama ba ga musulmai a fadin kasar.

Sultan yace: “Hijabi hakkin mu ne ba wai dam aba. Ba alfarma bane a gare mu. Hakkin mu ne. “Kuma muna amfani ne da kundin tsarin mulkin Jumhuriyyar Najeriya da ya bayar da daman yin bauta.

 “Shi yasa bamu takura wa kowa dake son yin bauta yanda yake so ba.”

KU KARANTA KUMA: Gwamnati ta sanar da sabon kudi da aka yanke ma dukkan makarantun gwamnati

Ya kara da cewa: “Kasar Najeriya kasa ce da ake addinai da dama, ba wai addini day aba. Kuma a matsayin ta na kasa mai addinai da yawa, dolene mu bari ko wani addini ta ci gaba a yanda take ba wai mu take hakkin juna ba, wanda yake nufin cewa dole a bari nayi addini na kamar yanda da na yarda da umarnin da Al-Qur’ani mai girma ba wai wani abu ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel