RIO 2016: Dan Nigeria ya yi kisa a wasan Dambe

RIO 2016: Dan Nigeria ya yi kisa a wasan Dambe

-Najeria ta yi rawar gani a wasan Dambe

-Dan wasan Damben Najeriya ya yiwa abokin karawarsa kwaf daya

-Ajagba ya samu zuwa mataki na gaba a wasan Dambe

A wasannin da ake yi na tsalle-tsalle da guje-guje na Olympics a Rio ta kasar Brazil, Najeriya ta yi rawar gani a wasan Dambe, a inda Efe Ajagba ya doke abokin karawarsa da ga kasar Trinidad & Tobago a turmin farko na wasan.

RIO 2016: Dan Nigeria ya yi kisa a wasan Dambe
Efe Ajagba bayan da ya doke abokin karawarsa Paul a karawarsu

Efe ya doke Nigel Paul ne a cikin dakikoki 23 kacal, a rukunin masu nauyin 91 kilogiram na gasar, wacce ake yi a halin yanzu a birnin na Rio na wannan shekara ta 2016.

Dan wasan daga Najeriya, wanda shi ne kadai ya ke wakiltar kasar a wasan Dambe na Olympics, ya nunawa abokin damben nasa cewa, ruwa ba sa’an kwando ba ne, wanda a turmin farko ya yi masa kwaf daya a wasan mai zagaye ko turmi sama da biyar.

Dan dambe Ajagba mai rike da kambin wasannin motsa jiki na Africa na shekarar 2015, yana kuma rike da lambar azurfa ta wasannin motsa jiki na kasashe renon Ingila, wanda aka yi a Glasgow ta kasar Britaniya a shekarar 2014.

Wannan karawar na nuna cewa Efe na iya ciwowa Najeriyar lambar zinare a inda ya samu zuwa mataki na kusa da na kusa da na karshe a inda zai  kara da Ivan Dychko daga Kazakhstan a ranar Alhamis 15 ga watan Agusta.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel