Matasan jam’iyar PDP sun kai wa dan majalisa hari

Matasan jam’iyar PDP sun kai wa dan majalisa hari

Wani dan majalisar jihar Yobe mai suna Abdullahi Adamu Bazuwa ya shad a kyar bayan daruruwa matasan jam’iyar PDP sun kai masa hari a karamar hukumar Potiskum.

Matasan jam’iyar PDP sun kai wa dan majalisa hari

Ana zargin matasan magoya bayan korarren shugaban jam’iyar PDP Ali Modu Sheriff ne, matasan sun far ma dan majalisan ne don zargin rashin tabuka komai cikin shekara guda da ya kwashe a majalisar jihar da su keyi masa.

Jaridar Leadership ta ruwaito dan majalisar dake wakiltar Potiskum na kan hanyar sa ta zuwa akwatin zabe na mazabar Bare Bari/Bauye Lelai don sa ido akan zabukan jam’iyar APC da ke gudana lokacin da matasan suka kai masa harin.

Wata majiyan gani da ido Mallam Isah Dafa yace matasan sun iso wurin suna ta ihun ‘Ba ma yi, karyane”. Majiyar tace matasan sun farfasa gilasan motar dan majalisar, sa’annan suka dinga jifar sa da rowan leda. Wasu daga cikin su sunce dan majalisar bai tabuka komai ba.

“maganar gaskiya, wannan mutumin bai taba bamu komai ba. Ba sa mana komai, don haka dole mu canja su daga sama har kasa, mu magoya bayan PDP ne.” inji wani daga cikin matasan. Harin ya kwashe awanni da dama ana ta yi, kafin yansanda da sauran jami’an tsaro su kawo dauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel