Hukumar NEMA sun hada yara 200 da iyayensu a Barno

Hukumar NEMA sun hada yara 200 da iyayensu a Barno

– Sama da yara 200 ne aka mayar muhallin su a jihar barno

– Yan kungiyan boko haram sun raba mutane da yawa da muhallin su.

Hukumar kawo agaji na gaggawa ta kasa NEMA ta hada yara sama da ya 200 da suka rikicin boko haram ya shafe su,da iyayen su.

Hukumar NEMA sun hada yara 200 da iyayensu a Barno

Game da rahoton, yawancin su yara ne , masu shekaru tsakanin 5 da 12 daga garuruwan Bama da Baga a Jihar Barno. An mika yaran zuwa da iyayensu bayan an gudanar da bincike na gane mutane a sansanin yan gudun hijra.

Yunkurin hada  iyayen da yaransu ya yiwu ne da taimako da hadin kai kungiyar agajin International Committee of the Red Cross (ICRC).

Shugaban ayyukan na ofishin Jihar Adamawa da Taraba , har yanzu akwai kimanin 165 da za’a kai gidajen su daga sansanin yan gudun hijrah guda 4 a Jihar Adamawa.

KU KARANTA : Yunwa na kashe mutanen da ke tsare a sansanin Boko Haram

A safiyar yau rundunar sojin najeriya sun kama wasu yan Boko Haram guda 5 wadanda suka kware a wajen birne bama bamai domin halaka mutane.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel