Yunwa baki san kowa ba: wata mai juna biyu ta saci N300

Yunwa baki san kowa ba: wata mai juna biyu ta saci N300

–Wata mata mai juna biyu mai suna Precious Ebuka ya shiga gidan makwabciyar ta da ke Abuja ta saci N300.

–Matar tace bakar yunwa ne ya tursasa ta tayi satan kudi N300

–Yan sanda sun bincike ta sun sami N300 a jikin ta

–Makwabciyar ta ce banda N300, an sace mata N80,000 a gidan.

–Wata kotun Grade 1 da ke zaune a Abuja ta ba Ebuka belin N5000 da kuma shaida mai kudin hakan

An gurfanar da wata mata mai juna biyu mai suna Precious Ebuka  a wata kotu da ke zaune a Abuja ta dalilin satan kudin makwabciyar ta domin ciyar da kanta.

Yunwa baki san kowa ba: wata mai juna biyu ta saci N300

Game da rahoton jaridar Vanguard , an tuhumi Ebuka da da laifin wuce gona da iri da kuma satan N80,000. Duk da cewan ta musanta hakan. Amma, Ebuka, wacce ke zaune a angwan idoma da ke dape Abuja,ta amince da cewan ta saci N300 a dakin makwabciyar ta.

Ta ce “na shiga ne saboda yunwa, ni ban ga wani N80,000 , ni N300 kawai na dauka”. An samu cewa yan sanda sun samu N300 a jikinta. Lauyan,zannah dalhatu ya fada ma kotun cewa Samuel Akoji ya kai karan zancen ofishin yan sandan life camp da ke Abuja.

Dalhatu yace : “Mai kawo kara da mai laifin mazauna gidan daya ne, yayinda akoji ya dawo gida ,ta lura da cewa an shiga mata daki saboda bah aka ta barshi ba da ta fita.

KU KARANTA : Yunwa ta sa ‘yan gudun hijira zama ‘yan kunar bakin wake

Ya ce mai laifin tayi amfani da wani mukulli irin na dakin Akoji domin kulla kofan

Game da cewar sa, laifuffukan ya saba bangaroran 348 da 288 na final kod. Amma , lauyan mai laifin, Charity Nwosu, ta nemi belin kuma ta tabbatar da cewa za’a biya belin. Daga baya Alkalin ,Alhaji Abubakar Sadiq ya baiwa Ebuka belin N5,000 da kuma shaida irin haka. Sadiq ya dakatar da karan ranan 7 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel