Antonio Conte ya hana ‘yan wasan Chelsea ciye-ciyen kwalama

Antonio Conte ya hana ‘yan wasan Chelsea ciye-ciyen kwalama

– An hana ‘yan wasan Kungiyar Chelsea cin kwalama.

– Antonio Conte ya kawo ka’idar cin abinci a Kungiyar.

– Conte dai na gudun a kara samun ‘yan wasan Kungiyar su yi nauyi su gaza gudu.

Antonio Conte ya hana ‘yan wasan Chelsea ciye-ciyen kwalama

 

 

 

 

 

 

 

Kocin kungiyar Chelsea, Antonio Conte ya bada umarnin dauke duk wani abincin kwalama da kuma lemu masu matukar iskar ‘gas’ daga kantunan Kungiyar. Jaridar nan ta ‘The Times’ ta Birtaniya ta rahoto cewa ‘yan wasan za su iske wannan labari ne suna dawowa daga wasannin yada zangon da su ke bugawa a Kasashen duniya. ‘Yan wasan na Chelsea za su dawo filin gidan na su ne a Ranar Alhamis dinnan 11 ga watan Agusta. Sai dai suna isowa za su ji labarin abin da ya faru na cewa, an hana ciye-ciyen kwalama a Kungiyar. Kocin na Chelsea dai na gudun kara faruwar abin da ya auku wancan shekarar da ta gabata a Kungiyar, wanda yayi tasiri wajen kwallon na Chelsea. A badi ‘yan wasan sun yi nauyi dalilin irin wannan ciye-ciyen, hakan kuma na kawo matsala a filin wasa.

KU KARANTA: MOURINHO YA BAYYANA LAMBAR DA POGBA ZAI BUGA

An dai saba ba ‘yan wasan kayan kwalama irin su gurasar ‘pizza’ bayan wasanni, Sai dai Antonio Conte yace ba za a kara hakan ba. Kocin na Chelsea yace bai kamata yan wasa su rika cin wani abinci mai danko daf da was aba, asali ma, kamata yayi ace suna cin abinci masu gini jiki da kuma kara lafiya idan ana shirin take wasa, hakan zai hana mutum ya cika tunbin say a ko kasa abin kirki a wasa. Domin dai ganin ‘yan wasan suna motsa jiki da kyau, Kocin ya kara lokacin horaswa a kowace rana.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel