Wata ta yadda dan ta a jihar Cross River (Hoto)

Wata ta yadda dan ta a jihar Cross River (Hoto)

Rahotannin da ke zuwa mana suna nuni da cewar wata mata a jihar Cross River ta yadda danta na cikin ta a wata coci dake garin Obudu.

Wata ta yadda dan ta a jihar Cross River (Hoto)

Ita dai matar mai suna Monica an ruwaito cewa ya gudu bayan ta yadda yaron a cocin kimanin watanni 5 kenan da suka wuce a garin Obudu. Ance dai matar ta ajiye yaron nata ne sannan kuma ta gudu bayan da ta nemi taimakon N1,000 daga hannun malamin cocin a farkon shekarar nan.

Shi kuma malamin cocin Rabaran Francis Agianpuye yace yaga yaron ne a harabar cocin bayan da uwar yaron ta gudu ta bar shi sannan kuma yace anga yaron ne tare da wasu yan kayan sa a cikin wata jaka a kusa da shi.

Rabaran Francis ya ci gaba da cewa bayan da ga hakan ne sai ya kai rahoto a ofishin yan sandan dake karamar hukumar ta Obudu. Daga nan ne kuma sai ya yanke shawarar daukar nauyin yaron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel