Mourinho ya bayyana gurbin da Pogba zai buga a Man Utd

Mourinho ya bayyana gurbin da Pogba zai buga a Man Utd

– Jose Mourinho yace Pogba da Carrick za su buga tsakiya.

– Sai dai Pogba a Juventus ya fi sabawa da ‘yan wasa uku a tsakiya.

– Mourinho yace su Schneiderlin da Herrera za su yi amfani.

Mourinho ya bayyana gurbin da Pogba zai buga a Man Utd

 

 

 

 

 

 

Kocin Man Utd ya bayyana yadda zai yi amfani da sabon dan wasan da ya saya kan makudan kudi har fam miliyan £90 a cikin fili. Mourinho ya bayyanawa BT sport cewa dan wasa Pogba zai buga tsakiya ne tare da dan wasa Michael Carrick. Pogba dai ya koma Kungiyar ne daga Juventus kan kudin da ba a taba ganin irin sa ba a tarihin sayayyan dan wasa. Pogba dai ya bar Man Utd ne shekaru hudu da suka wuce lokacin Sir Alex Ferguson yana kocin Kungiyar. Man Utd dai ta buga tsarin wasan 4-2-3-1 ne a wasan da ta buga da Leicester City a Gasar cin kofin Community Shield, an dai ga dan wasa Pogba ya kasa yin abin kirki sa’alin da Faransa tayi amfani da wannan tsari a wasan karshe na EURO 2016. Sai dai Kocin Man Utd Jose Mourinho yace shi tsarin da zai yi amfani da shi kenan a Kungiyar.

KU KARANTA: WASU YAN WASAN MAN UTD SUN BAR KUNGIYAR

Mourinho yace da BT Sport: “Muna da Carrick, mutum dan shekara 34 ko 35, yana da tabbas, yana kuma da tunani. Carrick ya san tsakiya, ya san kwallo” Jose Mourinho yace: “Muna kuma da su Schneiderlin, da Herrera, sun sa Premier League. Idan kuma ana maganar lamba 10 akwai Juan Mata, muna da Mkhitarya, ga kuma Rooney (wata sa’in)” Game da Pogba kuwa, Mourinho yace: “Yana da karfi sosai, yana kuma iya tare kwallo, sannan kuma ya raba ta. Kuma dai ya san raga, don ya iya cin kwallo, Pogba yana aika kwallo gaba, muna da masu raba kwallo, sai dai ba mu da masu yawo da ita, wannan sai su Pogba”

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel