Yadda aka yi Pogba ya zama dan wasa mafi tsada

Yadda aka yi Pogba ya zama dan wasa mafi tsada

– Paul Pogba ya koma Man Utd kan kudin da sun kai Naira Biliyan 45 (Na kudin Najeriya)

– Ana kamanta shi da Tsohon dan wasa Patrick Viera wajen karfi.

–Dan wasan ya bar Man Utd ne a baya saboda rashin buga wasanni.

Yadda aka yi Pogba ya zama dan wasa mafi tsada

 

 

 

 

 

 

 

 

A da ne ake raina bakar fata wajen kwallo kafa, yau ga dan bakar mace ya zama mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya, Pogba ya kafa tarihi inda Man Utd ta komo da shi daga Juventus kan kudi fam miliyan £105 (wannan daidai yake da Naira Biliyan 45). Da can ana kira san ‘Paul the Octapus’ saboda sharba-sharban kafafun sa, musamman idan yana gudu. Ana kamanta Pogba da Viera dan Kasar Faransa wajen yanayin wasan sa. An haifi Paul Labili Pogba a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 1993 a garin Lagny- sur-Marne, Seine-et-Marne na Kasar Faransa. Iyayen sa mutanen Kasar Guinea ne, yana kuma da yayyi maza ‘yan biyu masu suna; Florentin and Mathias, watau Pogba ne gambon su. Su kan su yayyun nasa yan wasan kwallon kafa ne, daya na bugawa Kungiyar St. Etine ta Faransa, daya kuma na can Kungiyar Partick Thistle ta Kasar Scotland.

KU KARANTA: POGBA YA ISO KUNGIYAR MANCHESTER UNITED

Paul Pogba ya fara buga kwallon kafa ne tun yana dan shekara 6 a Kungiyar US-Roissy-en-Brie da ke kusa da garin su, daga baya ya koma bangaren U-13 na Kungiyar, har aka yi masa kyaftin. Bayan nan ne kuma sai Pogba ya koma Kungiyar Le Havre, wannan ne Kungiyar farko da ya soma, ya kuma jagoranci Kungiyar ta gama ta biyu a shekarar. A shekarar 2009 ne Pogba ya bar Le Havre zuwa Man Utd, wannan abu ya kawo ‘yar sa-in-sa tsakani. Nan ne fa dan wasa ya koma Kungiyar Man Utd, ya shiga cikin sahun ‘yan matasa.

 

Za mu cigaba nan gaba

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel