Leicester City tyi watsi da tayin Arsenal akan Riyad Mahrez

Leicester City tyi watsi da tayin Arsenal akan Riyad Mahrez

Zakarun gasan firimiya a bara, Leicester City ta yi watsi da tayin pan miliyan 30 da Arsenal tayi ma dan wasanta Riyad Mahrez.

 

Leicester City tyi watsi da tayin Arsenal akan Riyad Mahrez

Mahrez dan kasar Algeria ya kasance jigo ne a kungiyar da ya taimaka mata wajen lashe gasar ta firimiya a karon farko a tarihin kungiyar, inda ya zura kwallaye 17 wanda hakan yayi sanadiyyar zamansa gwarzon dan wasa a bara. A cewar jaridar L’Equipe ta Faransa, Arsenal zata kara kudi a cinikin dan wasan.An samu labarin Mahrez kansa na sha’awar zuwa kungiyar Arsenal.

kungiyar Leicester ta sayi Mahrez ne a kan kudi kalilan pan 350,000 daga kungiyar Le Havre a watan janairu 2014, kuma ya nuna bajinta matuka a gasar firimiya. Za’a iya tuna abokin wasan Mahrez, Jamie Vardy ya nuna sha’awarsa ta komawa Arsenal, wanda saura kiris, amma daga bisani cinikin bai kaya ba. A yanzu dai dan kasar Ingilan ya kara rattafa hannu a sabon kwantaragi a kungiyar Leicester.

Asali: Legit.ng

Online view pixel