Anyi ma barawo dan Najeriya dukan tsiya a Ghana

Anyi ma barawo dan Najeriya dukan tsiya a Ghana

Wani dan najeriya mai suna Damilare ,wanda ke ikirarin ya karanci fanin injiniya a jami’ar obafemi awolowo kuma mazaunin Abuja yaci matsiyaciyar duka bayan anyi masa zindir haihuwar mamana a kasar Ghana ta dalilin aikin bera.

Anyi ma barawo dan Najeriya dukan tsiya a Ghana

Game da wani dan shafin facebook ,Annybrown Ahanmisi wanda itace ta fara bada gargadi akan yaron a watan da ya gabata akan yaron na cewa damilare wanda aka fi sani da‘jerryboidasaint’ a shafin instagram  ya sace gwal din ‘yar uwarta ,da kudin ta ,saboda haka mutane suyi hattara da shi.

KU KARANTA : Wani Mai gidan haya ya rataye kansa a Ibadan

Barawo baya arin halinsa. Bayan ya sace wa yar uawr Anny abubuwa, ya arce kasar Ghana domin cigaba da yaudaran mutane amma a wannan lokaci yayi rashin sa’a, an yi ram da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel