An kama wata gyatuma da laifin fashi da makami

An kama wata gyatuma da laifin fashi da makami

-‘Yan sanda sun damke wata gyatuma mai shekara 54 da laifin fashi da makami

-Daya daga cikin gungun ‘yan fashin ya amsa laifin cewa yan da hannu a fashin da aka yi

-‘Yan fashin su addabi mazauna yankin tun cikin shekara 2015

An kama wata gyatuma da laifin fashi da makami
Gytumar da aka kama tare da gungun 'yan fashi a Lagos

Rundunar ‘yan sanda shiyya ta 2 mai shalkwata a jihar Lagos ta yi holin wasu ‘yan fashi da makami da suka kware wajen tare manyan motoci a sassa daban-daban na jihohin Ondo, da Oyo, da Ogun da kuma Lagos.

A rahoton da Jaridar Punch ta buga ta ce, a cikin ‘yan fashin har da wata gyatuma mai shekara 54 da haihuwa mai suna Bola Ajayi, an kuma kama ta ne a yankin Ilupeju a Lagos ta na sayen kayan sata, zargin da ta karyata tana mai cewa, ba ta san ‘yan fashin ba sai dai ta taba sayen katan 100 na abin sha daga wurin dayansu.

Rundunar ta ce jami’anta sun cafke sauran ‘yan fashin da suka hada da Olanrewaju Gbadamosi dan shekara 33, da Lukman Akinola dan shekara 33,  da Dele Rotimi dan shekara 37,  da Taiwo Olabode dan shekara 38, da Uche Anthony dan shekara 27; da kuma Taiwo Ayodele dan 27.

‘Yan sanda sun kuma wasu gano bindigogi biyu kirar gida, da wata guda daya ta boge daga gungun ‘yan fashin da suka je fashi a wani otal a Ore a jihar Ondo.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel